Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, a matsayin jarumi saboda karbar faduwar zaben da ya yi a shekarar 2015

hoto: Twitter @atiku
- Atiku ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewar mutum ne da giyar mulki ke bugarwa da kuma riko da ra’ayin rikau
- Kazalika, Atiku ya zargi Shugaba Buhari da fakewa da siyasa domin cigaba da mulkin soja ta hanyar matsawa ‘yan jam’iyyar adawa da sunan yaki da cin hanci da rashawa.
A ranar Litinin ne tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mutumin dake cikin mayen giyan mulki tare da yin riko da ra’ayin rikau.
Kazalika, Atiku ya yaba wa tsohon shugaban kasa Jonathan tare da bayyana shi a matsayin jarumi saboda karbar kayen da shugaba Buhari ya yi masa a zaben shekarar 2015.
Sai dai wadannan kalamai na Atiku sun jawo masa raddi daga ‘yan Najeriya dake biye dashi a shafinsa dake dandalin sada zumunta na Tuwita.
Wasu daga cikin masu mayar da raddi sun nuna fushinsu a kan maganganun da Atiku ya fada a kan shugaba Buhari tare da fadin cewar yana sukar shugaban kasa ne saboda ya takura wa mutanen da suka saci kudin gwamnati a baya.

“Yanzu muna fama da mulkin tsohon soja, mai ra’ayin rikau dake cikin mayen giyar mulki. Mun san ba zai bar mulki ta hanya mai sauki ba kamar yadda tsohon shugaban kasa Gooluck Jonathan ya karbi kayen da aka yi masa a shekarar 2015 ba,” in ji Atiku.