Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martinin kan kiraye-kirayen da ake masa wajen ganin ya gudanar da sahihin zabe karkashin shugabancinsa a shekarar 2019.
Muhammadu Buhari (Shugaban kasan Najeriya) wanda yanzu haka na can a birnin Beijing na kasar China ya ce ko kadan baya tsoron a gudanar da zaben 2019 kan doron gaskiya da adalci ba tare da magudi ta kowacce fuska ba, domin kuwa shi kansa ya amfana da sahihin zabe da aka gudanar na shekaran 2015.
Da ya ke zantawa da al’ummar Najeriya mazauna kasar China, Muhammadu Buhari ya ce zai yi dukkannin abu mai yiwuwa wajen ganin ‘yan najeriya sun samu abin da suka zaba a babban zaben na badi(2019).
Mabanbantan bangarori kama daga na cikin kasar da kuma na ketare ne ke ci gaba da kir aga shugaban na Najeriya wajen ganin ya yi tsayuwar daka don gudanar da zabe mai inganci a dai dai lokacin da ya rage watanni bakwai al’ummar kasar su kada kuei’unsu.