Atiku Ne Shugaban Nijeriya A 2019 - Ekweremadu

atiku ne shugaban kasa a 2019 inji Ekweremadu

Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, Ike Ekweremadu, ya mika skakon taya murnarsa ga tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, a bisa nasarar daya samu na lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a garin Fatakwal.


Ekweremadu ya kuma taya sauran ‘yan takarar da jam’iyyar PDP murnar gabatar da taro mai tsafta ba tare da wani matsala ba.” ya lura da cewa, yadda aka gudanar da zaben yana da matukar mahimmanci don kuwa dukkan ‘yan takarar da suka fito daga jam’iyyar PDP sun cancanci shugabancin kasar nan baki daya.
Sanata Ekweremadu na mayar da martani ne dangane da sakamakon zaben fidda gwanin da jam’iyyar ta gunadar inda aka zabi tsohon shugaban kasa a matsayin wanda zai fuskanci shugaba Buhari na jam’iyyar APC a zaben da a za yi a shekarar 2019.





A sanarwar da mai bashi shawara a bangaren watsa labarai, Uche Anichukwu ya sanya wa hannu, Ekeremadu ya ce, lallai a hakin yanzu tsohon mataimain shugaban kasa Atiku Abubakar ne sbugaban kasa ma jira gado a Nijeriya. Ekweremadu ya kuma kara da cewa, “Ina mai bin sahun ‘yan Nijeriya da ‘yan jam’iyyarmu wajen taya Alhaji Atiku Abubakar murna, dan takarar jam’iyyarmu kuma shugaban kasar Nijeriya mai jiran gado da yadda Alla a 2019.


Wannan lamarin yana da matukar mahimmanci ga jam’iyyar PDP da kuma kasa baki daya, mafi mahimmanci a nan shi ne an gudanar da zaben ba tare da wani magudi ba, ina kuma yaba wa jam’iyyarmu tare da kwamitin shirya taron a bisa shirya taran da ba a taba yi irinsa ba a tarinin siyasar kasar nan.

Wannan yana kara nuna mana cewa, a halin yanzu jam’iyyarmu ta farfado da tsarin dimokradiyya a cikin gida tare da gudanar da zabe a cikin mutunci da kaunar juna, ina kuma bukatar dukkan ‘yan jam’iyya na su ci gaba da haka, ta haka ne zamu sau tabbacin nasarar cin zaben 2019 ba tare da wani mastsala ba.
Mataimakin shugaban majalisar dattijain ya kuma bayyana cewa, lamarin ceto Nijeriya ya fi karfi dukk wani mutum kuma wani abu ne da PDP ba za ta ba ‘yan Nijeriya kunya ba.

Sanatan ya kuma ce, wannna nasara da aka samu a zabbukkan da aka gudanar wanda aka yi ba tare da wani kofari daga dukkan bangare ba ya nuna cewa, tuni ‘yan Nijeriya suka dawo daga rakiyar jam’iyyar APC sun dawo bayan jam’iyyar PDP don dawo wa da kasa cikakkiyar tsarin dimokradiyyar daya kamata don kuma samun ci gaba a dukkan fannonin rayuwa da tttatalin arzikin kasa.

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne