Wani rikakken Shehi ya gano cewa Atiku zai yi mulki a 2019
Limamin wani coci mai suna KKDM a cikin Jihar Ebonyi, Emmanuel Chukwudi ya taba fitowa ya bayyanawa Duniya cewa Atiku Abubakar ne zai lashe zaben 2019. Malamin ya bayyana wannan ne a wata hudubar sa a baya.
Wannan Bajimin Malami yayi wannan jawabi ne tun kwanakin baya a lokacin da babu wanda yake tunanin cewa Atiku zai kai labari. Dama dai a baya, babban Malamin na Kirista ya taba gano cewa Atiku zai tsere daga Jam’iyyar APC.
Yanzu dai wannan hangen da Malamin yayi game da Atiku na nema ya zama gaskiya inda tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya samu tikitin takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP. Atiku zai kara ne da Shugaba Buhari a zaben 2019.
Shehin Malamin dai ya gargadi manyan Sanatocin kasar irin su Bukola Saraki da Dino Melaye a wancan lokaci da cewa ana shirya masu makarkashiya a Jam’iyyar APC. Yanzu haka dai dukkan su sun tsere daga APC sun dawo PDP.
Dazu dai kun ji cewa Sanata Dino Melaye ya bayyana wanda zai lashe zaben 2019 tsakanin Atiku da Buhari inda yace Shugaban kasa Buhari zai tattara kayan sa ya koma Daura a shekara mai zuwa.