ALBISHIRINKU MUTANEN JIHAR ZAMFARA

ALBISHIRINKU MUTANEN JIHAR ZAMFARA



Daga Datti Assalafiy
Maigirma shugaban 'yan sandan Nigeria Alhaji Ibrahim K. Idris yayi garambawul ga jami'an 'yan sandan Nigeria reshen jihar Zamfara ta hanyar canza kwamishinan 'yan sanda na jihar tare da maye gurbinsa da sabon kwamishinan 'yan sanda CP Zanna Ibrahim.

CP Zanna Ibrahim kwararren jarumin 'dan sanda ne wanda ya kafa tarihi wajen yaki da ayyukan ta'addanci da barayi 'yan fashi da makami, yana da basirar aikin 'dan sanda sannan bashi da tsoro kuma bai yarda da wargi ba.



Wannan dalilan ne ya sa Maigirma shugaban 'yan sandan Nijeriya zabo shi ya kai shi jihar domin ya tunkari babbar matsalar da ta addabi jihar Zamfara na yawaitar ayyukan masu yin garkuwa da mutane.

Tsohon shugaban 'kasar Nigeria Goodluck Jonathan lokacin da yake mulki ya taba sanyashi cikin wani kwamiti daga fadar shugaban 'kasa domin su gudanar da kwakkwaran bincike akan satar da akayi na 'danyen man fetur saboda kwarewa da CP Zanna Ibrahim yake dashi akan ilmin tsaro da binciken manyan laifuka.



Insha Allahu ni dai ina kyautata masa zato zaija daga sosai da manyan masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar Zamfara, kuma na tabbata a sanin da na masa duk wanda yake da hannu wajen taimakawa barayi a jihar Zamfara sai yayi binciken sirri ya bankadosu kuma ya kama su.
Hakika yana bukatar addu'ah, na farko muyi addu'ah Allah Ya karfafi zuciyarshi, sannan mu tayashi da addu'ah Allah Ya tsareshi daga dukkan makirci da sharrin 'yan kwangila.
Muna fatan Allah Ya masa jagora Ya nuna masa hanya mai sauki da zaibi ya tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar Zamfara Amin


Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne