ALHERIN ALLAH YA KAI GA JAN GWARZO SHUGABA BUHARI
Daga Datti Assalafiy
Wannan sabon Alkalin Alkalai na Nigeria (CJN) Justice Ibrahim Tanko Muhammad Malami ne masanin addinin musulunci, Mahaddacin Qur'ani ne tsantsa, ya rubutu Qur'ani da hannunsa, kwararre ne a harcen larabci gashi kwararren 'dan Boko digiri uku (Phd) yake dashi a karatun lauya, yana da lambar girmamawa na CFR
A Mahaifarsa dake garin Doguwa karamar hukumar Giade Jihar Bauchi akwai wani babban masallaci dake bakin hanya, shi ya gina masallacin, kuma duk watan azumi shi yake tafsirin Qur'ani Maigirma a masallacin
Tabbas yanzu Baba Buhari ya samu CJN, bai da wasa, kuma yana da zafi, ga sanin Allah da riko da addinin musulunci tsantsa, ina mai tabbatar muku jama'a ku sa ido kuga aiki wajen wannan bawan Allah, zuwansa kan wannan kujera rahama ne daga Allah domin Allah Ya taimakawa shugaba Buhari wajen yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria
Hankalin makiya addinin Allah kuma makiya cigaban Nigeria da Manyan jibga-jibgan barayin Nigeria maciya amana wadanda sukaci amanar Nigeria da 'yan Nigeria, da wadanda suka mayar da ta'addancin Boko Haram hanyar neman kudi; hankalinsu yayi mummunan tashi bisa nadin da shugaba Buhari yayiwa wannan bawan Allah a matsayin sabon babban alkalin alkalai na Nigeria
Jama'a ku dubi wani rahoto da BBC Hausa ta wallafa a shafinta na facebook, ga (screenshort) sun kawo rahoton cewa gwamnatin Amurka da Birtaniya sun nuna damuwarsu akan nadin da shugaba Buhari yayiwa wannan bawan Allah, sunce wai suna shakkun a samu sahihin zabe a Nigeria
Jama'a kuji zancen banza daga 'kasashen banza, ina ruwansu da zaben Nigeria, ko dai suna so su tabbatar mana cewa akwai boyayyen shirin da sukayi tsakaninsu da tsohon alkalin alkalai kan abinda ya shafi zaben Nigeria? tunda yanzu an koreshi boyayyen shirin nasu ya rushe kenan!,
Bayan haka, na ga tsageri 'dan ta'adda shugaban kungiyar masu rajin kafa 'kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu wanda yake zaman mafaka a haramtacciyar 'kasar Isra'ila ya bayyana cewa canza sabon CJN yana da nasaba da kokarin murda zaben 2019 wanda gwamnatin Buhari ke shirin aiwatarwa
Shekaran jiya na karanta rahoton da babban makiyin arewa da musulunci bakin arne bamaguje kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama na Nigeria
Mr. Femi Fani Kayode ya wallafa a shafinsa na Facebook (ga screenshort) a dalilin canza alkalin alkalai da shugaba Buhari yayi, nan take Femi Fani Kayode ya addinantar da al'amarin, ya fito ya caccaki shugaba Buhari, haka itama kungiyar kiristoci ta CAN ta addinintar da lamarin
Amma Alhamdulillah ina da niyyar nayi raddi da zaran na samu lokaci, kawai sai naga babban Malaminmu Ash-sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo har yayi raddi kamar haka:
HALAYYAR MUNAFURCI ABIN TAKAICI NE:
1. A ranar 20/2/2014 Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi wa Gwamnan babban bankin Nigeria Malam Sanusi Lamido Sanusi daga jihar Kano korar wulakanci daga kujerarsa, amma kuma karkatattun 'yan kudu, da masu akidar kin Musulmi da 'yan kanzaginsu na cikin gida da wajen Nigeria ba su ce kome ba; ba su ce an saba ka'ida ba, ko kuwa an nuna bangaranci da saba tsarin mulkin Nigeria ba!!
2. A cikin watan May 2012 National Judicial Council ta yi muraja'ar dakatarwar da aka yi wa Justice Ayo Salami daga jihar Kwara daga kan mukaminsa na President of the Nigerian Courts of appeals sannan ta yi umurnin a maida shi a kan mukaminsa nan take, to amma Goodluck Ebele Jonathan ya ki mayar da shi a kan mukamin nasa, kuma abin takaici karkatattun 'yan kudu, da masu akidar kin Musulmi da 'yan kanzaginsu na cikin gida da wajen Nigeria ba su ce kome ba; ba su ce an saba wa tsarin mulkin Nigeria, ko an nuna bangaranci ba!!
3. Don Allah in banda yin awu da sikeli biyu menene zaisa a soki Shugaban kasa Buhari don ya yi aiki da umurnin kotun da'ar ma'aikata ya dakatar da Justice Onnoghen daga kan mukaminsa har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci a gaban alkalin da'ar ma'aikata?? ~Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Don Allah jama'a mu yiwa kawunan mu tambaya, wai shin mai yasa mutanen kirki a Nigeria basu soki wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka na canza sabon CJN ba? amma me yasa hankalin mutanen banza, masu kaunar ruguza Nigeria ya tashi a kan wannan batu?
Tabbas akwai wata kullalliya a 'kasa, kuma daga dukkan alama Allah Ya wargaza kullalliyar da makiya suka 'kulla
Allah Madaukakin Sarki muke roko Ya taimaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan wannan babban aiki da ya sanya a gaba na yin yaki da manya-manyan masu cin hanci da rashawa da maciya amana a cikin wannan Kasa tamu Nigeria. Ameen.
Tags
siyasa
