ANYI KIRA GA MAJALISA A GAGGAUTA TSIGE BUHARI
Shugaban jam’iyar African Democratic Congress (ADC) Cif Ralphs Nwosu ya yi k'ira ga majalisar tarayya ta gaggauta tsige shugaban k'asa Muhammad Buhari ta nad'a shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki a matsayin shugaban k'asa.
Ralphs Nwosu ya nemi majalisa su tsige Buhari ne a cewarsa ya yi karan tsayen ma tsarin mulkin Najeriya wajen dakatar da babban Alk'alin Alk'alai Walter Onnoghen.
Wannan jawabi ya fito ne ta bakin babban Sakataren yad'a labarai na k'asa a jam'iyar ADC d'in Yemi Kolapo.
Kolapo ya bayyana cewa ya zama dole majalisa su tsige Buhari da Osinbajo su nad'a Abubakar Bukola Saraki saboda yadda suke cigaba da keta dokar kasar nan.
Tags
siyasa
