Tsohon karamin ministan tsaro a zamanin mulkin gwamnatin PDP data gabata, karkashin shugabancin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Musliu Obanikoro ya bayyana ma kotu cewar shi da kansa ya kai ma tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose dala miliyan biyar daga kudin makamai.
Obanikoro ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 21 ga watan Janairu a gaban Alkalin babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Ikeja na jahar Legas inda yace shine wanda Kanal Sambo Dasuki ya bashi dala miliya biyar ya kai ma Fayose a shekarar 2014.
Kanal Sambo Dasuki ne tsohon mashawarcin Jonathan akan harkokin tsaro, shi kuma Fayose ya tsaya takarar gwamnan jahar Ekiti a shekarar 2014, don haka Dasuki ya aika masa $5m daga cikin kudin da aka ware na sayo makamai don yaki da Boko Haram, da nufin yayi yakin neman zabe.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Fayose a gaban kotu a ranar 22 ga watan Oktobar shekarar 2018 inda take tuhumarsa da laifin satar kudi naira biliyan 6.9, tare da kamfaninsa, Spotless Investment Ltd. Sai dai ya musanta tuhumar, hakan tasa kotu ta bada belinsa akan kudi Naira miliyan 50.
Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs ya gabatar da shaidarsa ta biyar a gaban Alkali a ranar Litinin, shaidan kuwa shine tsohon minister Obanikoro, inda ya tambayeshi zai iya tuna inda yake a shekarar 2014? Shi kuma ya kada baki yace masa shine ministan tsaro na jaha a shekarar.
Ya cigaba da cewa “A lokacin da zaben gwamnan jahar Ekiti na shekarar 2014 ya karato, Fayose ya kirani yana tambaya ne ko akwai wani sako da Sambo Dasuki ya bani na kawo mai? Sai na fada masa cewa babu wani sako a kasa, amma zan tambaya masa. Daga bisani sai Dasuki ya tabbatar min akwai sakon da zai bani na kai ma Fayose.
“A ranar 13 da 16 na watan Yuni na shekarar 2014 aka zuba kudaden cikin asusun banki, kuma kudin sun fito ne daga ofishin Sambo Dasuki, sai na tambayi Fayose ko ta yaya yake son kudin, sai yace min yana son wasu a dala, wasu kuma a naira.
“Haka na tattara masa kudin dana canza zuwa naira naira biliyan 1.2 a cikin wata motar daukan kudi na kai masa sashin jirage masu zaman kansu dake filin sauka da tashin jiragen sama na Ikeja jahar Legas, inda wani dan aiken Fayose Agbele ke jirana, daga nan aka wuce da kudin zuwa Ekiti.
“Bayan kwana biyu kuma na hadu da Fayose a wani otal dinsa mai suna Spotless, inda na bashi sauran kudin dake a dala, dala miliyan biyar ($5,000,000) wannan ya faru ne kwanaki uku kafin zaben gwamnan.” Inji shi.
Sai dai da aka tambayeshi daga ina aka samu kudin, sai Obanikoro ya bayyana ma kotu cewa Dasuki ne kadai zai iya bayyana inda ya samo wadannan kudaden, amma dai daga ofishin asusun ofishin Dasuki suka fito.
Bayan kammala bayaninsa ne, sai Lauyoyin wanda ake kara suka nemi kotu ta dage sauraron karar, daga bisani Alkalin kotun Mojisola Olateregun ya amince, inda yada karar zuwa ranat 14 ga watan Feburairu.
