BARAYIN TATTALIN ARZIKIN NIGERIA KUN SHIGA UKU!

BARAYIN TATTALIN ARZIKIN NIGERIA KUN SHIGA UKU!
Sabon babban alkalin alkalai na Nigeria Chief Justice of Nigeria (CJN) Mai shari'ah Ibrahim Tanko Muhammad yace; daga yanzu duk wata shari'ah da ake yinta a kotu wacce take da nasaba da cin hanci da rashawa, nayi alkawarin za'a kammalata a yanke hukunci a tsakanin kwanaki goma sha biyar (15 days) kacal Alhamdulillah wannan babban nasara ne kuma babban cigaba ga 'yan Nigeria a bangaren dakile cin hanci da rashawa wanda yake matukar illata 'kasar ta fuskoki da dama Muna rokon Allah Ya taimaki sabon babban alkalin alkalai Allah Ya bashi dukkan nasara da taimako da yake nema Amin

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne