FIRE SERVICE SUN ZUBAWA MUTANE RUWA ATARON BUHARI



Tab dijam: Saboda zafi da yawan jama'an a taron APC na Borno, sai da jami'an haya-haya suka taimaka da ruwa 2 hours ago 2600 views by Humaira Samaila Yayinda shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Borno, dandazon jama'a masoya shugaban sun cika farfajiyar Ramat Square dake qwaryar Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Saboda yawan jama'a a wajen taro, zafi ya yi yawa wanda ka iya kawo hallakan rayuwa. Hakan ya sabbaba zuwan jami'an haya-haya domin taimakawa da ruwa domin watsawa mutane ko zafin zai ragu. Ku tuna cewa mun fada muku cewa gwamnatin jihar Borno ta sanar da ranar Litinin, 20 ga watan janairu a matsayin ranar hutu ga dukkan ma'aikatan ta saboda zuwan da shugaba Buhari zai yi jihar domin yin kamfe din tazarcen sa a tare da magoya bayan sa a ranar. Majiyar mu ta sanar da mu cewa gwamnatin jihar ta Borno ta bayyana a cikin sanarwar bayar da hutun cewa ta yi haka ne domin ta baiwa kowa damar yin tururuwa domin zuwa tarbar shugaban kasar idan ya zo. Kalli hotunan:





Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne