KUNGIYAR ASUU TA CIMMA MATSAYA DA GWAMNATIN TARAYYA

Gwamnatin tarayya a zamanta na yau da kungiyar malaman jami'a sun cimma matsaya.
Da ya ke ganawa da ‘yan jaridu yau a Abuja, ministan kwadago, Criss Ngege ya ce gwamnatin tarayya ta cimma matsaya ga dukkan bukatun kungiyar daga ciki har da na biyansu Nera Biliyan15.4 na domin biyan albashinsu da aka rike.
Ya ce gwamnatin na kuma kokarin yadda za ta fitar musu biliyan 20 domin biyan basukan alawus alwus na malaman.
Shugaban kungiyar, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce ba za su ce komai ba dangane matakin da suma dauka har sai kwamitin sun zauna da kungiyar.
Ya kara da cewa, bayan kammala zaman kungiyar ASUU ne za su sanar da matakinsu na janye yajin aikin da suke ko sabanin hakan.
Kusan wata uku ke nan da tafiya yajin aikin kungiyar wanda sai a yau suka cimma fahimtar juna. Yanzu dai a na sauraro daga bangaren kungiyar domin janye yajin aikin.
Tags
Education