WASU MATASA SUN WANKE INDA ATIKU YAYI GANGAMI A LOKOJA
Wankan Tsarki: Matasa A Lokoja Sun Share, Sun Wanke Inda Atiku Yayi Gangamin Neman Zaben Sa
Wasu gungun matasa mun samu labarin cewa sun yi gangami sun yi aikin gayya wajen sharewa tare da wanke in dan takarar shugabancin kasar Najeriya a karkashin tutar jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi taron kamfe din sa a garin Lokoja.

Hotunan matasan dai wanda ya yadu a kafafen sadarwar zamani yana dauke ne da matasan rike da tsintsinya yayin da kuma wasu suke dauke da jarakunan ruwa suna wankewa tare da share inda jam’iyyar ta PDP da dan takarar ta suka gudanar da gangamin kamfe din su.
Tags
siyasa