AN KAMA BUBA GALADIMA





Bayanai daga iyalen Dan hamayyar nan Alhaji Buba Galadima sun shaida wa BBC cewa an kama Buba din ranar Lahadin nan.
Wani makusancin sa ya ce suna zargin jami’an tsaron farin kaya ne na DSS suka kama Buba da rana jim kadan bayan ya fita daga gidansa.
Wani makusancin dan siyasar a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabacin Najeriya a jam’iyyar PDP da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun tura wakilansu zuwa ofishin DSS domin bincika dalilin kama Buba Galadima.
Sai dai har kawo yanzu babu wani bayani daga hukumar ta DSS kan zargin kama jigon na hamayya.
A ranar Asabar, Festus Keyamo da ke magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Muhammmadu Buhari ya yi kira a kama Buba Galadima, bisa zargin yan shirin bayyana sakamakon zabe na boge.
Buba Galadima dai shi ne shugaban R-APC wani bangare da suka balle daga jam’iyyar APC, kuma yana cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar da ke takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP.


source:

BBC HAUSA

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne