Bukola Saraki ya fadi zabe

Yakubu Dogara da Bukola Saraki

Shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki ya sha kaye a Kwara ta tsakiya da yake wakilta a majalisa.

Sakamakon zaben da aka tattara kafin hukumar zabe ta sanar, sun tabbatar da cewa Saraki ya fadi a dukkanin kananan hukumomi hudu da yake wakilta.

Dan takarar APC ne Ibrahim Oloriegbe ya kayar da Saraki a yankin Kwara ta tsakiya da ya kunshi kananan hukumomin Ilori ta yamma da Ilori ta Kudu da Ilori ta gabas da kuma Asa.

Bukola Saraki na jam'iyyar PDP wanda kuma ya jagoranci yakin neman zaben Atiku ya samu kuri'u 30,075.

Ibrahim Oloriegbe na jam'iyyar APC kuma ya samu kuri'u 51,531 daga cikin jimilla 91,130 da aka kada.


Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne