JAMI'AN KWASTOM SUNYI BABBAN KAMU

JAMI'AN KWASTOM SUNYI BABBAN KAMU
Jami'an tsaron Kwastom Zone 'A' Lagos sun samu nasaran kama mayayyakin 'yan sanda anyi fataucinsu wanda aka loda a cikin wata mota kirar Toyota Sienna za'a fitar da kayayyakin zuwa wani guri daga birnin Lagos Babban jami'in Kwastom a shiyyar Zone A, Area Controller Muhammed Aliyu yace sun kama mutum daya wanda aka samu da safarar kayan na 'yan sanda, ya kara da cewa babban barazana ce ga tsaron Nigeria, domin anyi shirin mika kayayyakin 'yan sandan ne ga batagari, masu garkuwa da mutane ko kuma 'yan ta'addan Boko Haram Kayan da aka kama sun hada da: -Uniforms -Tear gas -Ranks -Belts -Berets -Police badges -Identity cards Da yake karin bayani Area Controller Muhammad Aliyu yace cikin kayayyakin akwai badges na 'yan sanda masu matsayin Sergeant da Inspector, amma katin shaidar aikin 'dan sanda (Identity cards) da suka kama an bugasu ne batare da sunan 'dan sandan dake kan katin ba, batagarin da sukayi safarar kayan suna so da zaran an wuce da kayan sai su saka sunayen mutanen da sukeso suyi amfani da katin shaidar aiki na 'yan sanda A cikin kowani bandir na kakin 'yan sanda da suka kama, bandir daya za'a iya dinkawa 'yan sanda kaya guda 10, yace 'yan Nigeria sun jima suna zargin akwai 'yan sanda na bogi, bayan kayan 'yan sanda da suka kama anyi fataucinsu akwai har da adduna, shin 'yan sandan Nigeria suna amfani da adda ne?, kun taba ganin 'yan sandan gwamnati suna amfani da adda? to wannan yunkurin wasu batagari ne suke so suyi amfani da wannan damar a daidai lokacin da ake tunkarar babban zabe na kasa ini Area Controller Muhammad Aliyu Zone 'A' Lagos Muna rokon Allah duk wasu miyagub mutane da basa neman zaman lafiya a Nigeria Allah Ya shiryar dasu, idan ba zasu shiryu ba Allah Ya tona musu asiri

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne