JIRAGEN YAKIN NIGERIA SUNYI RUWAN WUTA AKAN TAWAGAR BOKO HARAM
Maimagana da yawun rundinar sojin saman Nigeria Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana sanarwan cewa wasu jiragen leken asiri sun leko tawagar 'yan Boko Haram/ISWAP sun taru suna tattaunawa a wani yanki da ake kira Kolloram dake yankin Tafkin Chadi a jihar Borno
Bayan jiragen leken asirin sun gano 'yan ta'addan shine sai aka tura manyan jiragen yaki Alpha Jet dauke da manyan bama-bamai da roket sukayi ruwan wuta akan tawagar 'yan Boko Haram din
'Yan ta'addan sunyi amfani da bindigar da ake harbo jirgin sama wato Anti-Aircraft (AA) don su harbo jirgin amma ba su kai ga nasara ba, jiragen yakin sun jefa musu manyan bama-bamai kuma an hallaka adadi mai yawa daga cikin 'yan ta'addan tare da rushe gine-ginen da sukayi a yankin
Muna rokon Allah Ya karawa rundinar sojin Nigeria nasara akan 'yan Boko Haram Amin
Tags
Tsaro