MASU SATAN AKWATIN ZABE KUN SHIGA UKU BURUTAY

Rundunar Sojan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin Buhari akan barayin akwatin Zabe



 Rundunar Sojan kasan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari daya bayar na bindige duk wani ko wasu da aka kama suna kokarin sace akwatin zabe a babban zaben kasar da zai gudana a mako mai zuwa. 

A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya bada wannan umarni yayin wani taron jam’iyyar APC na musamman daya gudana a babban ofishin jam’iyyar na kasa dake babban birnin tarayya a Abuja, sai dai batun ya janyo cecekuce a tsakanin yan Najeriya.

 Yayin da wasu ke ganin wannan mataki na shugaban kasa yayi daidai, wasu kuma na ganin matakin yayi tsauri dayawa, a cewarsu ba’a hukunta barawon akwatin zabe da bindiga, daga cikin wadanda suka koka kan umarnin na Buhari akwai jam’iyyar PDP, Sanata Shehu Sani, Yakubu Dogara da sauransu.

 Sai dai da take tsokaci game da wannan umarni na shugaban kasa, rundunar Sojan kasa ta bayyana shirinta da kuma manufarta na dabbaka umarni ba tare da wata wata ba, matukar shugaban kasa ne ya bayar da ita. 

“Idan har babban kwamandan askarawan Sojin Najeriya ne ya bayar da wannan umarni ga rundunar Sojan kasa, ku sani tabbas zamu aiwatar da wannan umarni gaba dayansa dari bisa dari ba tare da wani kwana kwana ba.” Inji Kaakakin rundunar, Kanal Sagir Musa.

 Sai dai kafin wannan zance na shugaban kasa, rundunar Sojan kasa ta bayyana cewa zata jibge dakarunta a cikin shirin ko-ta-kwana amma ba’a kusa da akwatin zabe ba don gudun tsoratar da masu zabe, amma da wannan umarni, sai dai muyi kira ga masu shirin satan akwatin zabe dasu shiga taitayinsu.

Me Zakace Game Da Wannan Hukuncin Da Baba Buhari Ya Yanke.

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne