MAKIYA ZAMAN LAFIYAR NIGERIA SUN TAYAR DA SABON RIKICI A JIHAR KADUNA

A sanar da matafiya, yankin Kajuru da Kachia na jihar Kaduna babu lafiya kar abi hanyar
Wanda yake taimakawa gwamnan jihar Kaduna da yada labarai Mr. Samuel Aruwan ya bayyana wa manema labarai sabon rikicin da ya barke a garuruwan Kajuru da Kachia
Da safiyar yau Talata wasu mahara 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba, sun kaddamar da sabon hari a garin Maro dake karkashin karamar hukumar Kajuru da wani yanki na karamar hukumar Kachia jihar Kaduna
An samu asarar rayuka da kone konen gidaje da dakunan bauta a dalilin sabon harin, yanzu haka an tura karin yawan jami'an tsaro yankin don shawo kan sabon rikicin da ya barke
Na ga wasu jaridu suna cewa wai wannan sabon hari da aka kaddamar na daukar fansa ne akan kisan kiyashin da aka yiwa fulani a garin Kajuru sati biyu da suka gabata, inda aka hallaka fulani sama da dari aka kone musu gidaje aka kashe musu dabbobi
Wato dai ana kokarin bayyanawa duniya cewa fulani ne suka kaddamar da wannan sabon harin tun kafin bincike ya tabbatar, amma saboda rashin adalci ba'ayi saurin bayyana kisan da aka yiwa fulani sati biyu da suka gabata ba
Allah muke roko Ya kawo zaman lafiya a Kudancin Kaduna da Nigeria gaba daya Amin
Tags
Tsaro