![]() |
| Sheik Muhammad Auwal Adam Albani Zaria |
Muhammad Auwal Adam Albaniy Zariya (Satumba 1960 - Feb, 2014) wani masanin Islama ne mai ilimi a Hadith. Dokar Islama(Shari'a), Aikin Jarida, Sadarwar Kasuwanci da ICT. Ya kasance mai fasaha a rayuwarsa ta farko wanda ya kira kansa 'kwararren tela' (Specialized Tailor). Shi ne malami na farko da ya rubuta kalmar "Salafiyyah" kama daga kan Malamai har daliban Ilimi gaba daya na kasarmu Najeriya. Malam Albani, malamai da yawa suna ikrarin cewa shine babban Malamin Salafiyya da kasar ta taba samu.
DAN GUNTUN BAYANAI DANGANE DASHI:
Ranar Haifuwa: 6th Rabi'unith Thani, 1379 A.H daidai da 27 Satumba 1960
Ya Rasu: 01 Fabrairu, 2014 (A 53).
Ƙasarsa: Najeriya.
Qabila: Hausa / Fulani.
Addini: Islama.
Aqeeda: Sunni Salafiy.
Babban sha'awarsa; Karatun Hadisi da ICT.
Allah ya jikanshi da Rahma, ya kuma gafarta masa.
Amin.
