Wata mata mai suna Iyangida Ibrahim ta haifi jarirai hudu maza biyu mata biyu a babban asibitin kwanciya na Hadejia.

Matar mai kimanin shekaru 37 a duniya ta haifi wadannan jarirai da sanyin safiyar wannan rana ta Laraba.
Mijin matar Malam Ibrahim Adamu ya ce zuciyar sa na cike da farin ciki dangane da wannan kyauta da Allah madaukakin sarki ya ba shi.
A baya dai an yiwa matar awu inda da likita ya shaida musu cewa tana dauke da jarirai uku, amma sai ga shi ta haifi ya' ya hudu.
Jami'ar da ke lura da dakin karbar haihuwar a asibitin ta Hajiya Hama Ibrahim ta ce wannan ne karon farko da aka haifi jarirai hudu a asibitin.
Yanzu haka dai mahaifiyar tare da jariran na cikin koshin lafiya.
Tags
Al'ajabi