Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana soki Shugaba Muhamadu Buhari bisa nasarar da ya samu na lashe zaben shugabancin kasa na 2019 da aka gudanar a ranar 23 ga watan Satumba kuma aka sanar da sakamakon zaben a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Sheikh Gumi ya koka kan yadda Buhari ya yi gadarar cewa shine zai lashe zaben tun kafin a fara kirga kuri'u da al'umma suka kada.
Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Dr Gumi Source: Twitter Kamar yadda muka samu daga Daily Nigerian, Sheikh Gumi ya ce, "Tun kafin a kirga kuri'u, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi imani 100% cewa shine zai lashe zabe. Ta yaya ya san shine zai lashe zaben duba da cewa kan 'yan kasar a rabe ta ke kuma ana fama da talauci da fatara?
Tags
siyasa