- Zakzaky ya umarci mabiyansa akan karsu zabe Atiku da Buhari a zabe mai zuwa.
Maganganu sun yi ta yawo kan yiyuwar shigan 'yan Shi'a babban zabe me zuwa a kasar nan da za'a fara ranar 16 ga watan biyu musamman ganin yadda a baya sukan kauracewa shiga harkokin zaben ciki kuwa hadda takara da jefa kuri'a.
Haka a 'yan kwanakin nan wasu rohatanni sun bayyana cewa almajiran na Zakzaky da ke da yawa a wasu daga jahohin arewacin kasar nan zasu bada dukkan kuri'unsu ga Alhaji Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin Jam'iyar Adawa ta PDP.
A ranar Asabar 26/01/2019, wasu daga makusantan Shaik Ibraheem Zakzaky sun ziyarce shi a wajan da ake tsare da shi sannan ya yi magana kan zantukan da ake yadawa kansu akan zaben inda suka ce yace su kauracewa zaben da za'a yi.
Wasu daga wadanda suka ziyarci Zakzaky din sun ambato shi yana cewa “To mu muna zabe ne? Ina ruwan mu da zaben su. Kuma ma mu ai ba'a sanmu da hargitsi ba, idan ma haka ne. Su kansu wannan al'ummar sun yi mana shaida akan cewa mu ba masu hargisti bane” inji shi.