: An gano asirin da magauta su ka yiwa El-Rufa’I asiri a Kaduna 
An gano wata gora da ke dauke da wasu kayan kulumbuto da wasu rubutun surkulle da aka yi da ajami a wasu makabartu a unguwannin Sabon Kawo da Unguwar Dosa.
An gano wata gora da ke dauke da wasu kayan kulumbuto da wasu rubutun surkulle da aka yi da ajami a wasu makabartu a unguwannin Sabon Kawo da Unguwar Dosa.
Daga cikin rubutun surkullen da aka yi a jikin wata gorar duma an rubuta sunan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Ruf’ai da Haruna Aliyi Chakis a cikin likkafani a kulle sannan aka binne a makabartar.
Ana zargin wasu magauta gwamnan da shirya ma sa wannan kulumbuto domin ya mutu kafin a gudanar da zaben gwamnoni na jiya ko kuma ya fadi. A zaben da aka gudanar jiya a Kaduna, kun ji cewar a sakamakon zaben jihar Kaduna ya nuna cewa ‘dan takarar PDP Honarabul Muhammad Isah Ashiru Kudan ya doke jam’iyyar APC a akwatin sa da ke Mazabar sa a cikin Kudan. APC ta samu kuri’a 33 ne yayin da PDP ta samu 284.
An gano asirin da magauta su ka yiwa El-Rufa’I asiri a Kaduna Source: Twitter Malamin zaben da yayi aiki a rumfa ta 007 da ke cikin Unguwar Kofar Fada a karamar hukumar ta Kudan ya bayyana wannan. Shi ma dai ‘dan takarar na PDP ya sha kashi hannun gwamna Nasir El-Rufai a ta sa mazabar a Kaduna.
Tags
siyasa