Atiku Ya Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharudda
Dan Takarar shugabanchin kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya gabbatar da wasu sharudda Guda Biyar da ya ke son Shugaba Muhammadu Buhari ya cika kafin ya Aminche da Gwamnatinsa.
Atikun ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da kwamitin zaman lafiya a karkashin jagorancin Tsohon Shugaban kasar nan na Milkin Soja Abdulsalami Abubakar.
Sharuddan kuwa sun hada da cewa.
• Bude Asusun Bankunan ‘yan jam’iyyar Adawa da aka rufe.
• Janye sojoji daga wuraren zabubbukan da za a yi nan gaba.
• A rika tantance masu zabe kafin a fara kada kuri’u a sauran zabubbukan da su ka yi saura.
• A saki duk ‘yan siyasar da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba.
• Haka kuma, Atiku ya bukaci hukumar zabe ta bude shafin yanar gizonta, ta yadda duk jam’iyyun siyasar da ke takara za su iya shiga su duba yadda abubuwa ke gudana.
Wadannan sune Sharuddan da Atiku ya Gindaya, Ana sa ran kwamitin zaman lafiyar ya gabatar dasu ga Shugaba Muhammadu Buhari a Ganawar dasukayi dashi a Yau din nan.
Shin yaya kuke kallon wadannan Sharuddan
Tags
siyasa
Lalle wannan sharudda ba abun anincewa bane, saboda daman wannan shina manufar gombatin PDP idan sun ci zabe. Dan haka shugaba Buhari bazai laminci wannan ba.
RépondreSupprimerEh wannan zancenka haka ne
Supprimer