KUNGIYAR KAFA KASAR BIAFRASUNA ROKON SHUGABA BUHARI YA CIRESU DAGA JERIN KUNGIYOYIN TA’ADDANCI
KUNGIYAR KAFA KASAR BIAFRAWORLD NEWS

SUNA ROKON SHUGABA BUHARI YA CIRESU DAGA JERIN KUNGIYOYIN TA’ADDANCI
Datti Assalafiy Posted onMarch 1, 2019
Kungiyar matasan Inyamurai “The Ohanaeze Ndigbo Youth”, tana roko ga shugaba Buhari da ya cire haramtacciyar kungiyar ‘yan ta’adda ta Inyamurai masu rajin kafa Kasar Biafra wato INDIGENOUS PEOPLE OF BIAFRA (IPOB) karkashin jagorancin ‘dan ta’adda Nnamdi Kanu sunyi kira ga shugaba Buhari daga cikin jerangiyar kungiyoyin ta’addanci a Nigeria
Wanda yayi wannan kiran shine shugaban kungiyar ta matasan Inyamurai Mr Mazi Okechukwu Isiguzoro, yace akwai kuskura cikin matakin da gwamnatin Buhari ta dauka na saka kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda
Don haka yake kira ga shugaba Buhari da ya musu afuwa ya cire kungiyar IPOB daga cikin jerangiyar kungiyoyin ta’addanci
Idan ba’a manta a karshen shekarar 2017 gwamnatin Nigeria ta ayyana kungiyar ‘yan rajin Kafa Kasar Biafra a matsayin kungiyar ta’addanci sakamakon daukar makami da sukayi don su kafa sabuwar Kasarsu ta Biafra
Tags
Tsaro