Komai Ta Fanjama Fanjam A Cewarsa.

Tsohon ministan shari’a a zamanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Mohammed Adoke, wanda ya kwashe shekaru hudu yana buya tare da tserema hukumar EFCC, ya kammala shirin dawoa Najeriya, komai ta fanjama fanjam a cewarsa.



Adoke ya sanar da niyyarsa ta dawowa gida Najeriya ne a wata hira da yayi da jaridar Premium Times, inda yace zai dawo Najeriya a tsakanin watanni Yuli da Satumba domin fuskantar duk ma abinda zai sameshi.

Majiyar ta ruwaito hukumar EFCC ta dade tana farautar Adoke da nufin jin bahasin rawar daya taka wajen badakalar cefanar da rijiyar danyen man fetir na Malabu akan dalan amurka biliyan 1, fiye da naira biliyan 360 kenan.

Amma a bangare guda kuma Adoke ya sha musanta wadannan zarge zarge, wanda hakan yasa wata kotu a karkashin jagoran Mai Sharia Binta Nyako ta wankeshi daga tuhume tuhumen da ake yi masa, inda tace bai aikata wani lafi ba.

Adoke yace ya bar Najeriya ne da nufin kara karatu a birgin Hague, amma daga bisani ya samu labarin ana nemansa ruwa a jallo a Najeriya, hakanan ya tsaya an duba lafiyarsa a kasar waje, sa’annan har ya fara rubuta littafinsa kan rawar daya taka a mukaminsa na Minista.

Daga karshe Adoke ya bayyana Najeriya a matsayin wata kasa mai wuyar sha’ani, kasar da bata godiya ga wadanda suka yi mata bauta, suka sha wuyarta, inda yace duk da irin kokarin da yayi ma Najeriya, amma abinda za’a saka masa dashi kenan.

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne