- Wasu fusatattun dalibai sun kone asibitin kwalejin Polytechnic na jihar Osun
- Daliban su n kone asibitin ne saboda mutuwar wani dalibi, inda suke zargin ya mutu saboda rashin samun kulawa
A yau Asabar dinnan ne daliban kwalejin Polytechnic ta jihar Osun, suka sanyawa gurin karbar magani na makarantar wuta akan mutuwar wani dalibi a makarantar.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana rahoton cewa masu gadin kwalejin ne suka yi kokarin hana wutar yaduwa zuwa wasu wuraren, inda suka samu suka kashe ta cikin gaggawa.
Rahotanni sun nuna cewa, wani dalibi mai suna Aminu Hammed, wanda yake karatun difloma a bangaren kimiyya, ya fadi a dakin jarrabawa jiya Juma'a inda aka yi kokarin garzayawa dashi zuwa asibitin makarantar, inda daga baya ya ce ga garinku nan.
Daliban da suka fara zanga-zangar yau Asabar dinnan da safe, sunyi zargin cewa babu ma'aikata a asibitin lokacin da aka kai Hammed da zasu ceto rayuwarsa.
A lokacin zanga-zangar, daliban sun sanyawa motar asibitin wuta, sun kone magunguna da kayyaki da yawa a asibitin.
Tags
fitina
