MAKIYA NIGERIA SUNA YIWA KASAR MUGUN TANADI

MAKIYA NIGERIA SUNA YIWA KASAR MUGUN TANADI
Kungiyar masu rajin kafa 'kasar Biafra (IPOB) sun ware ranar 16-2-2019 a matsayin ranar da zasu gudanar da zaben ficewa daga tarayyar Nigeria (Referendum), shugaban kungiyar ne Nnamdi Kanu ya bayyana hakan Jama'a kun fahimci makircin? sun saka ranar da zasuyi zaben ficewa daga Nigeria a ranar da za'a gudanar da zaben shugaban 'kasa, kuma wannan zabe na Referendum zabe ne sahihi wanda majalisar dinkin duniya ta yarda dashi ga duk wani yanki da yakeso ya fice daga wani yanki a cikin 'kasa ta hanyar zabe ba tare da tayar da hankali ba A yanzu haka Nnamdi Kanu ya baro haramtacciyar 'kasar Isra'ila inda aka bashi mafaka ya iso zuwa birnin London domin ya tattauna akan wannan kuduri da suke so su cimma tare da goyon bayan turawa Kwanaki an ruwaito Obasanjo yace shima zai goyi bayan inyamurai su balle daga Nigeria su kafa sabuwar 'kasarsu ta Biafra idan har aka kyale shugaba Buhari ya zarce Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Nigeria Femi Fani Kayode ya wallafa a shafinsa na twitter da facebook cewa idan har aka kyale shugaba Buhari ya zarce zai goyi bayan wargaza Nigeria su ma Yarbawa zasu kafa 'kasarsu ta Oduduwa a cewarsa Tsohon jagoran tsagerun Neja Delta Mujahid Dokubo Asare ya bayyana a faifan Video yana cewa dole su hada karfi da karfe su tabbatar sun fice daga Nigeria a wannan zabe da za'a gudanar a Nigeria, ina da videon yanzu haka kusan mintuna 10 Jama'a idan kun lura da yadda wasu manyan kasashen turawa da kuma wasu manyan makiya zaman lafiyar Nigeria hankalinsu ya tashi game da koran tsohon alkalin alkalai wanda shugaba Buhari ya dakatar, za'a iya fahimtar boyayyen shirin da akayi dashi akan zaben Nigeria da kuma makomar ita 'kasar tamu Nigeria, don naga wani rahoto da aka fitar ance jami'an DSS sun nadi muryansa ana kitsa makirci dashi akan zaben Nigeria Bari na bada wani misali: Duk wanda ya nutsu sosai yayi nazari akan zazzafar siyasar da ake yinta a Nigeria, idan akayi zabe 'yan adawa zasu iya kin amincewa da sakamakon zaben, turawa zasu iya fitowa su goyi bayan 'yan adawa, zasu siyasantar da lamarin ta yadda har majalisar dinkin duniya zata shigo, abinda ya faru a wata 'kasa a wayi gari anyi haka a Nigeria domin wallahi Buhari ne ba'aso ya zarce ta kowani hali Kuma ina mai tabbatar muku da wannan bayani kowa ya rubuta ya ajiye, idan akayi zaben shugaban 'kasa dakyar ne idan ba'a kai ga zagaye na biyu ba, kuma ratar da APC zata baiwa PDP a wannan babban zabe da za'ayi kalilan ne, Buhari ba zai taba samun yawan kuri'ar da ya samu a 2015 ba, ku tuna wani rubutu da nayi mai taken AKWAI MATSALA FA inda nayi bayanin yadda masu jefa kuri'a zasu karkasu Akwai masu makauniyar soyayyar Buhari daga cikinmu wadanda idonsu ya rufe ba zasu iya fahimtar bayanin gaskiya da ake ba balle suyi amfani da shawarar da ake bayarwa, to irin wadannan masu makauniyar soyayya ba Buhari suke taimako ba, daga can sama kuma ana yaudarar shugaba Buhari basa fada mishi gaskiyar abinda yake faruwa, amma ina da cikakken yakinin cewa zasu tuna dani a ranar zabe idan Allah Ya kaimu Kar mu yaudari kanmu da ganin yawan jama'ar da APC take tarawa a gurin yawon kanfe suma PDP suna tarawa Shawaran da zan bamu mu masoya shugaba Buhari shine kowa ya tabbata ya karbi katin zabensa, idan da hali Limaman masallatai na khamsussalawat da na Juma'a suyi kira ga jama'ar musulmi dare da rana kowa yaje ya karbi katin zabensa ya adana, sannan a fadakar da mutanen arewa ko da wasa kar ayi yunkurin tayar da fitina, mu saka a ranmu cewa ko dukanmu akayi mukaji zafi a jikinmu muyi hakuri mu yafe, kar mu goyi bayan duk wani yunkuri na tayar da hankalin 'kasa. Sannan mu dage da addu'ah da kuma wayar da kawunan junanmu. Allah Ka bamu zaman lafiya a Nigeria Allah Ka bamu shugabanni na gari masu tausayin talakawa da gaskiya da rikon amana Allah Ka mana maganin wadanda basa son mu zauna lafiya a Nigeria Amin

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne