SAURA QIRIS AFARA DAKON FETUR A AREWA

SHUGABA BUHARI YA CANCANCI YABO DA GODIYA
Wannan shine hotunan kwangilar aikin tonon rijiyoyin man fetur wanda shugaba Buhari ya bayar ake gudanar da aikin a boye a yankin kogin Kolmani dake kauyen Barambu karamar hukumar Alkaleri Jihar Bauchi Aikin tonon rijiyoyin man fetur din yana gudana ne a karkashin jagoranci babban darakta a ma'aikatar man fetur na 'kasa Maikanti Baru, kuma shugaba Buhari da kanshi yace ya jagoranci aikin, bai yarda a baiwa wani ba sai daraktan, kuma a boye ake gudanar da aikin kamar yadda watannin baya na dinga fitar da bayanai a kai, shugaba Buhari yana so kwatsam sai dai a wayi gari jama'a suga an fara fitar da danyen man fetur daga arewa An kusa kaiwa ga gaci, Jihar Bauchi tana dab da fara fitar da danyen man fetur , saura kiris tsagerun yankin Neja Delta su dena yiwa arewa gori akan man fetur insha Allah, wannan babban ginshike ne da zaisa arewa ta tsayu da kafafunta Baba Buhari Muna godiya Allah Ya taimakeka Ya baka dukkan nasara da kake nema Amin

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne