MUTANEN SHEKAU SUNSHA WUTA A JEJIN SAMBISA

MUTANEN SHEKAU SUNSHA WUTA A JEJIN SAMBISA
Maimagana da yawun rundinar sojin sama na Nigeria Air Commodore Ibikunle Daramola ya fitar da sanarwan cewa jirage masu leken asiri sun gano wasu gungun 'yan ta'addan Boko Haram da suka taru a tsakiyar jejin sambisa, shine sai aka aike da jiragen yaki suka zuba musu ruwan wuta daga sama, an hallaka adadi mai yawa na 'yan ta'addan Babu shakka yau Abubakar Shekau zaiyi kwanan bakin ciki, don dama shi kam tashi ta kare saura ya shigo hannu ne kawai ya rage masa, Allah Ka wulakanta Shekau da masu tallafa masa ka tona musu asiri gaba dayansu Allah Ka karawa sojojin Nigeria nasara da taimako akan 'yan ta'adda

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne