SUN KAI SHI SUN BARO SABODA.........

SUN KAI SHI SUN BARO SABODA.........
Duk wani mai Shekaru 40 ko 30 zuwa Kasa bai taba ganin shugaba mai Farin Jini da Allah ya horewa Jama'ah Talakawa irin #Shugaba_BUHARI ba Amma kuma shine Shugaban da Talakawan suka shiga cikin Halin Ha'ula'i mafi muni ta banagaren Tattalin Arziki, da walwalan mutane musamman anan Arewa, shima da kan shi ya fadi haka da bakin shi a 2017, kana ji kana gani za'a sace ka fa! sai ankawo kudin fansa, kuma bantaba jin Wanda aka ce Gwamnati ta biya mishi ba dukda wannan Nauyin na kan Gwamnatin ne, duk wannan Talakawa sun sani amma kowa yayi shiru Saboda Soyayya, maganar Gaskiya wannan ba soyayya bace Me yasa? Saboda kwata kwata Shugaba BUHARI baida mashawarta Adalai a tattare dashi, Wallahi duk Basira da sanin makaman aikin ka mulkin Nigeria yafi karfin mutum daya 1 ko shi waye, dole sai an Taimaka maka, to shi baida su sai mugaye masu zuga shi suna hana shi aikin Alkhairi kuma idan aka zo kuka da shi ake yi ba su ba, domin shi muka zaba Duk wani Abu da Talaka zai ji Dadi ya samu Natsuwa da Aminci sun dauke shi akai sai suke tuttura shi cikin halaka ta yadda basa gaya mishi ainihin halin da Talakan ke ciki kullum sai karya suke mishi, ko jarida ce da ke dauke da koken Talakawa baza a yarda a kaita gaban shi ba, abun dai babu Tausayi a ciki Shi da kanshi ba dadin mulkin yake ji ba, zaka iya gane hakan ne kawai idan dama ka San shi, duk wata hanya da ake bi aji dadin mulki ayi NASARA wannan Shugaba bai biyo ta wajen ba, me yasa? Tun 2015 da Allah ya kawo shi yake fada da manyan mutane masu Daraja a cikin Kasa Wanda wasun su suna da hannu wajen samun mulkin da ya yi, maimakon koma menene a daura shi akan hanyar da za'a warware kowace matsala ta ruwan sanyi Tunda Siyasa ake yi ba QUR'ANI da SUNNAH ba, babu wata Gwamnati da zata taba yin Nasara akan mulki irin na Democracy Alhalin tana fada da Majalisan Dokoki (SENATE) da Mai'aikatan Shari'ah (JUDICIARY) babu yadda za'ayi ne ko kai waye domin idan babu su mulkin baya ciki A cikin Kasar nan muna kallo ake so akai shugaban Majalisa #Abubakar_Saraki gidan Yari saboda zargin bai bayyana kadarorin shi ba muna kallo aka je gidan Alkalai cikin dare aka ci mutuncin su wai ana zargin sun boye kudi a gida, Jama'ah siyasa akeyi fa, koda sunyi da gaske ana iya kauda kai aci wata riba koda Albarkacin Talakawan suci mana, wallahi Allah kadai ya isa yayi yadda yake so da mutane amma mutum dole ya kauda kanshi a wani wajen sannan ya zauna lafiya, babu mashawarta sai.......... BUHARI vs IMN BUHARI vs IPOP BUHARI vs Elites BUHARI vs Part of Poor masses BUHARI Gov't vs Labour BUHARI vs Part of JUDICIARY BUHARI vs US BUHARI vs England BUHARI vs EU Jama'ah' Me yasa a wannan zamani kana mulkin siyasa za kayi rikita rikita da wadannan? Ta ina za'a Bullewa wannan Hanyar saboda Allah? Ya Allah ka kawo mana sauki

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne