SABON SANARWA GAME DA KISAN JANAR IDRIS ALKALI

Rundinar 'yan sandan Nigeria reshen jihar Pilato ta fitar da sabon sanarwa na neman wasu mutane 'yan kabilar berom mutum sha-uku (13) ana nemansu ruwa a jallo game da kisan Manjo Janar Idris Alkali
Cikin mutanen da rundinar 'yan sandan ta fitar da sanarwan nemansu ruwa a jallo mutum 13, 12 daga cikinsu sun fito daga kauyen Dwei ne dake gundumar Du, mutum 1 cikon na 13 ya fito daga kauyen Gushen a karamar hukumar Jos ta kudu
Ga sunayensu kamar haka:-
-Kannan Nyam
-Solomon Gyang Jang
-Dustine
-Dung Deme
-Gyang Murrak
-Chuwang Samuel
-Nyam Samuel
-Dung Gbeh
-Daddy Dogo
-James Dung
-Gyang Dung
-Jay Boy
Maimagana da yawun rundinar 'yan sandan jihar Pilato DSP Mathias Tyopev yace; ayyana wadannan mutane da akayi a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo ya biyo bayan sabon bincike da rundinar 'yan sandan take cigaba da gudanarwa game da kisan Janar Idris Alkali, wanda hakan yasa ta gano suna da hannu dumu-dumu a ciki wajen kisan Janar din
Rundinar 'yan sanda reshen jihar Pilato tana rokon jama'a duk inda akaga wani mai suna irin na wadannan da aka lissafa a sama ayi kokarin kaiwa rahoto zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko kuma a kira wadannan nambobin waya kamar haka: 07059473022, 08038907662, 08075391844, 09053872296.
Jama'a a taimaka wajen yada sanarwa.
Muna rokon Allah Ya tona musu asiri a duk inda suka buya a wannan duniyar
Allah Ka sa kisan Janar Idris Alkali yayi sanadin kawo karshen ta'addancin berom a kudancin Jos Amin
Allah Ka jikanshi Ka kyautata makwancinsa Amin
Tags
Labarai