Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir-raaji'un
Duk Da Bashi Da Lafiya , Amma Ya Ce A Kawo Shi Ya Zabi Buharist , Da Yin Zaben Ba jimawa kadan Ya Ce Ga Garin Ku nan .

Wani mara lafiya mai suna Bashar Mamman, ya amsa kiran Ubangiji jim kadan bayan ya kada Kuri'arsa a Mazabarsa wadda kuma ita ce Mazabar Shugaban Kasa Muhammad Buhari.
Bashar mai shekaru 25 kafin yau ya kasance yana cikin Matsananciyar Rashin Lafiya, duk da Haka ya ce a kawo shi ya yi Zabe, wanda sai a keken marasa lafiya aka kawo shi yayi zabe da Misalin karfe 2 Saura na rana, Yana komawa Gida bayan ya Jefa Kuri'ar sa Karfe 6:30, ya ce Ga garinku nan.
Muna Rokon Allah ya yi masa Gafara.
Madogara Abokina Shai'ubu Abdullahi