- Dan takarar APC a mazabar Gombe ta Arewa ya lallasa na jam'iyyar PDP a karamar hukumar Kwami

Dan takarar kujerar mazabar Gombe ta Arewa a majalisar dattijai, Sanata Saidu Ahmed Alkali ya lashe zaben karamar hukumar Kwami da ke jihar Gombe. Ya lallasa babban abokin hamayuarsa, Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda shi ne gwamnan jihar mai ci a yanzu, da ke takara karkashin jam'iyyar PDP.
Yanzu yanzu: Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya sha kasa a karamar hukumar Kwami Source: Depositphotos Bisa rahotanni na sakamakon da aka wallafa na gundumomi 10 da ke karamar hukumar, Sanata Alkali na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 26, 795 yayin da Dankwambo ya samu kuri'u 14,019. Karamar hukumar kwami na daya daga cikin kananan hukumomi biyar na mazabar majalisar dattijan.