An dade ana zargin akwai takun saka tsakanin Gwamna Ganduje da Shiek Daurawa tun lokacin da malamin yayi huduba akan batun zargin da ake yiwa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na karbar cin hanci a wani fefen video inda malamin yayi kira ga gwamnan akan idan har yasan ya karbi cin hancin Dalar Amurka da ake zarginsa da ita to ya fito ya bayyanawa duniya gaskiya kuma ya nemi gafarar mutanen jihar Kano da kuma duk musulman duniya game da laifin.

Wannan furucin na Shiek Daurawa ya janyo cece-kuce Inda mutane ke yaba masa kan kalaman a gefe guda kuma magoya bayan gwamnan sukayi ta sukarsa suna kiraye-kiraye akan a saukeshi daga kujerarsa ta shugaban hukumar Hizbah wacce ke karkashin gwamnatin jihar Kano
A baya-bayan nan ma an hango Shiek Aminu Daurawa ya sake jagorantar wasu limaman jihar Kano suka kaiwa Senator kwankwaso ziyara da nuna goyon bayansu gareshi akan wasu kalamai da kwankwason yayi akan wasu Malaman kungiyar izala kwankwason yayi kalaman ne sakamakon zargin da yakeyi wasu Malaman kungiyar suna nuna goyon baya ga tsagin gwamna Ganduje sannan suna sukar tafiyarsa ta Kwankwasiyya
A yammacin yau ne muka samu rahoton bada umarnin garkame Ofishin Kwamandan na Hizbah, Inda ake zargin gwamnatin Kano da kokarin sauke Shehin malamin daga jagorancin hukumar Hizbah
Tags
siyasa
siyasa