[sabon Labari] INEC TAHADA CAKWAKIYA

Chakwakiya: INEC ta aika da kayan aikin zaben jihar Kebbi zuwa Kaduna bisa kuskure



Kwamishinan Zabe na Jihar Kebbi, Ahmad Mahmud ya ce anyi kuskuren kai wasu daga cikin kayayakin aikin na jihar Kebbi zuwa Jihar kaduna sannan wasu da ya dace a kai jihar Katsina an ka su jihar Katsina.

Mahmud ya yi wannan bayanin ne a yayin da ya ke hira da manema labarai bayan ya gama tantance kayayakin zaben a babban bankin Najeriya da ke jihar Kebbi inda ya ce "Biyu daga cikin fom EC 8D1 da EC 8E1 na jiha Kebbi suna jihar Kaduna yayin da na jihar Katsina kuma an kai su jihar Kebbi.

"Mun gano kuskuren ne a yayin da muke tantance kayayakin zaben kuma a halin yanzu ana hanyar dawo da su jihar Kebbi. "

Baturen zaben ya ce INEC reshen jihar Kebbi ta karbi dukkan kayayakin aikin zaben ta na zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya kuma za a fara rabar da su a ranar Laraba a kananan hukumomi 21 na jihar.
Ya ce an gama dai-daita dukkan na'urar card reader na jihar.

" A halin yanzu an gama dai-daita dukkan kayayaki aikin zabe masu muhimmanci na jihar Kebbi da na'urorin card reader kuma a gobe Laraba za mu fara rabar da kayayakin zabe masu muhimmanci "
Ya ce za a gudanar da zabuka a mazabun zabe 2,398 da rumfunan zabe 1,345 da rumfunan zabe 225 da ke jihar.

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne