Tsagerun IPOB Sun Sake Yunkurowa Da Batun Kafa Kasar Biyafara

A ranar Lahadi ne, Haramtacciyar kungiyar nan ta ‘yan asalin yankin Biyafara ta ce, ba da jimawa ba kasar ta Biafara za ta tabbata. 


Kungiyar ta bayyana hakan ne a garin Awka, Jihar Anambra, ta hannun kakakinta na yada labarai, Emma Powerfull.

Sanarwar kungiyar na cewa, “Al’ummar ‘yan asalin yankin Biafra da shugabannin su suna kara tabbatar da matsayin su a sarari ga duk mahankalta ‘yan Nijeriya da ma na Duniya, cewa batun kafa kasar Biafra, ba gudu ba ja da baya a kansa duk da yanayin jam’iyyun siyasun kasar Nijeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, “Yin zabe a Nijeriya aikin banza ne. Ba mu damu da sakamakon zaben da yake cike da aringizo a cikin sa ba, wanda suka kira wai da an yi zabe.

Tsabagen yanayin cin zarafin al’umma, tursasawa, kashe-kashe da shelanta sakamakon zabe na karya, da kuma irin farfagandar da aka rika yadawa a kan shugabanmu Mazi Nnamdi Kanu, da duk kungiyoyin zaman lafiya, ba za su iya dakatar da shawarar da muka yanke ba ta kafa kasar Biafra, nan ba da jimawa ba, inji su.

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne