Yanzu Yanzu Mutane 16 Sun Mutu A Hadarin Mota

Da duminsa: Mutane 16 sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota a jihar Kano



An samu asarar rayuka masu yawan gaske sanadiyyar wani mummunan hadari da ya faru a jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa kimanin mutane 16 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar hadarin Kimanin mutane 16 ne ake tunanin sun rasa ransu jiya Juma'a da dare, a wani hadarin mota da ya afku tsakanin wasu motoci guda uku, a kauyen Tukwi da ke kan hanyar Dambatta zuwa Daura da ke jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa, motocin da lamarin ya afku da su suna kan hanyar su ta zuwa karamar hukumar Daura da ke jihar Katsina, yayin da hatsarin ya afku. Wani Hakimi a garin Dambatta, Muhammad Jamil Dambatta ya shaidawa manema labarai afkuwar lamarin. Ya ce mutane 17 ne hatsarin ya shafa, a ciki akwai maza 14 da mata guda uku. 

Enregistrer un commentaire

Plus récente Plus ancienne